ABIN MAMAKI: Riƙaƙƙen ɗanbindiga ya dawo ba wa manoma kariya a Zamfara

Daga Sabiu Abdullahi

Wani abu da zai iya zuwa wa jama’a da yawa da mamaki shi ne yadda fitaccen dan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen addabar jama’a a arewacin Najeriya,.Dogo Giɗe, ya fara ba wa manoma kariya don su koma nima gonakinsu a jihar Zamfara.

A cewar wani rahoto na musamman da BBC Hausa ta wallafa a yau Alhamis, manoma a ƙananan hukumomin Tsafe, da Maru da ke Zamfara, da ma wani ɓangare na yankin ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina, sun shaida cewa sun zauna da Dogo Giɗen.

Sannan ya musu alkawarin kare su daga sauran gungun ƙungiyoyin ƴan bindigar da a baya suka hana su noma a gonakinsu.

Rahoton na BBC ya kara da cewa riƙaƙƙen ɗan bindigar ya koma gida Zamfara ne bayan dakarun Najeriya sun yi luguden wuta tare da lalata gidansa, da komawarsa ne kuma ya gargaɗi kungiyoyin ƴan bindigar da ke wadannan yankuna su daina kai wa jama’a hari da hana manoma noma, idan kuwa ba haka ba zai hakala su.

A cewar wani mazaunin yankin, ”Yana can gefen Babbar Doka da ke karamar hukumar Maru, iyayensa ne suka roke shi ya koma gida bayan harin da sojojin Najeriya suka kai gidansa, bayan ya koma ne ya yi wa sauran wannan kungiyoyin yan bindiga gargaɗi, yanzu haka ana zaune lafiya, manoma sun koma gona ba wata matsala, daga Magami za ka tashi ka tafi har Taketa, babu wata matsala, Dogo Gide na kare jama’a”

Yankin arewacin Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsaro wacce ta haifar da  koma baya ga bangarori da dama, daga ciki har da noma, wanda aka san yankin da shi.

More from this stream

Recomended