Abin da ya sa masarautar Kano ta soke hawan Nasarawa

Sarki Sanusi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Masarautar ta ce ta soke Hawan Nasarawa da hawan Dorayi saboda umarnin gwamnati da kuma kaucewa duk abinda zai iya jefa rayuwar jama’a da lafiyarsu cikin hadari

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta soke hawan Nasarawa da sarkin Kano yake gudanarwa duk ranar biyu ga sallah saboda dalilan tsaro.

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar Laraba ta ce ta samu bayanan sirri da suka nuna cewa akwai yiwuwar samun matsalar saba doka da oda yayin hawan na Nasarawa.

A duk ranar biyu ga salla ne dai Sarkin Kano yake gudanar da hawan na Nasarawa, inda a yayin hawan ya kan ziyarci fadar gwamnati, sannan ya zagaya wasu sassan birnin Kano.

Sanarwar wacce sakataren watsa labaran gwamna Abba Anwar ya sanyawa hannu an dauki matakin ne bayan taron masu ruwa da tsaki kan al’amuran tsaro a jihar ta Kano

Sanarwar ta ce tuni an sanar da “masarautar cikin birni matakin ksn rahoton na sirri da kuma soke hawan na Nasarawa.

A nata banagaren masarautar ta Kano ta ce ta samu wannan umarni daga gwamnati kuma ta janye hawan na Nasarawa da ma hawan Dorayi da ake gudanarwa ranar hudu ga sallah.

Sakataren masarautar ta Kano Malam Awaisu Abas Sanusi ya shaidawa BBC cewa masarautar ta soke hawan ne bayan samun umarnin gwamnati da kuma son tabbatar da zaman lafiya, da toshe duk wata dama da bata gari za su iya amfani da ita wajen cutar da al’umma.

An dai fara hawana Nasarawa ne tun lokacin da turawan mulkin mallaka suka ci Kano da yaki a 1909, inda sarki yake kaiwa baturen mulkin mallaka ziyarar gaisuwar salla sannan ya yi amfani da damar wajen kewaya wasu sassan birnin Kano, musamman yankunan da baki ke zaune.

Sai dai gabanin sanarwar soke hawan, gwamnatin ta aikewa masarautar Kano wata takarda inda take sanar da cewa gwamna ba zai samu halartar hawan Daushe ba kamar yadda aka saba saboda wasu dalilai.

Sanarwar wacce ta bulla bainar jama’a ta kuma shaidawa masarautar ta Kano cewa gwamnan ba zai samu damar karbar bakuncin Sarkin Kano ba a yayin hawan Nasarawa saboda wasu dalilai da ba a ambata ba.

To sai dai gwamnan da wasu manyan gwamnati sun jagoranci tawagogi zuwa hawan Daushe da sababbin masarautun da gwamnan kafa suka gabatar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wata sanarwa da sakataren watsa labaran na gwamna ya fitar ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa hawan Daushe a masarautar Bichi.

Shi kuwa mataimakin gwamnan na Kano Nasuru Yusuf Gawuna ya jagoranci wata tawagar zuwa hawan Daushe a masarautar Rano, yayinda shugaban majalisar dokokin jihar Kano Kabir Alhasan Rurum ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati zuwa hawan da aka gudanar da masarautar Karaye.

Shi kuwa sakataren gwamatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya jagoranci wata tawagar zuwa masarautar Gaya.

Sai dai babu wani wakilin gwamnati da ya halarci hawan Daushe da sarkin Kano Muhamad Sanusi II ya gabatar a ranar Laraba.

Sharhi daga Yusuf Ibrahim Yakasai

Masu fashin baki dai ba su yi mamakin da matakin na gwamnati na soke hawan na Nasarawa ba, da ma rashin halartar gwamnan Kano wajen hawan Daushe da aka yi a fadar sarkin Kano ba.

Dama tun kafin sallah an yi zaton cewa gwamnan na Kano ba zai halarci hawan na Daushe ba, kuma sai gashi hasashen masu cewa zai je Bichi ne domin hawan ya tabbata.

Wasu ma sun yi mamakin ganin yadda gwamnan ya halarci sallar idi a filin idi na Kofar Mata, wanda mai martaba sarkin Kano ne yake jagorantar sallar.

Masu irin wannan ra’ayi dai na ganin cewa rashin jituwar da ta fito fili tsakanin gwamnan Kano da Sarkin Kano tun bayan zaben 2019 za ta iya haifar da kowane irin lamari.

A ganin masu sharhi da dama matsalar rashin jituwar ita ce ta sa gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiri Karin masarautu hudu a Kano domin zama kishiyiyo ga masarautar Kano dake da girma da kasaita.

Image caption

Gwamnatin Kano dai na cewa babu sabani tsakaninta da masarautar Kanon

Tun bayan kirkiro masarutaun dai an ga yadda gwamnan Kano ya kulla kawance na kut da kut da Sarkin Bichin Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero kuma na hannun daman Sarki Sanusi ne kafin a nada shi sarkin Gaya.

Har yanzu dai gwamnatin Kano na cewa babu wani sabani tsakaninta da msarautar Kano, kuma ta kirkiri masarautun ne domin bunkasa ci gaba, to sai dai abubuwan da suke faruwa a zahiri sun nuna sabanin hakan.

Tun bayan nada sababbin sarakunan da Ganduje ya yi, gwmanan na Kano ya ziyarci duka masarautun sama da sau daya, musamman ma dai masarautar Bichi da gwamnan yake kai wa ziyara fiye da sauran.

To sai dai tun daga lokacin, Ganduje bai kai ziyara masarautar Kano ba. Hatta ma lokacin da aka yi saukar tafsirin da ake yi a fadar sarkin na Kano gwamna bai halarci saukar ba, wacce a bisa al’ada gwamnoni kan je.

Wani abu da yake kara fito da rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu, shi ne rashin halartar Sarki Sanusi II wajen rantsar da Gwamna Ganduje wa’adi na biyu, inda sauran sababbin sarakunan hudu gaba daya suka halarta.

Wasu bayanai da na samu daga wasu na kusa da gwamnati sun tabbatar min da cewa gwamnan Kano ya kullaci sarkin Kano saboda bai goyi bayansa ba lokacin da Ganduje ya nemi wa’adi karo na biyu a zaben 2015.

Majiyarta kara da cewa gwamnati tana da hujjojin da ke nuna cewa Sarkin bai so Ganduje ya sake cin zabe ba, sannan kuma ya taya dan takarar PDP Abba Kabir Yusuf yakin neman zabe a karkashin kasa.

To sai dai gwamnatin ba ta tabbatar da wannan magana ba a hukumance, sannan ita ma masarautar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ba kan wannan zargi.

Sai dai tun bayan zaben an lura da cewa takun gwamnatin Kano ya sauya dagane da Sarkin Kano da masarautar Kano.

Hakkin mallakar hoto
SALIHU TANKO YAKASAI

Bayan zaben ne majalisar dokokin Kano ta yi doka a kan kirkirar Karin masarautu kuma gwamna ya sa mata hannu, aka nada sarakunan, aka basu takarda, sannan aka basu sanda a cikin kasa da kwana bakwai, abinda wasu ke ganin an yi ne domin cimma wata manufa ta zuzgunawa sarkin Kano.

Sannan daga lokacin ne kuma hukumar karbar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta sake taso da binciken da ta taba yi kan yadda aka kashe kudin masarautar Kano bayan nada Sarki Sanusi, inda aka yi zargin cewa an kashe kudin ba bisa ka’ida ba tare da yin almabazaranci da kudin da ya haura Naira biliyan uku.

Masarautar ta Kano dai ta musanata zargin, inda tun a wancan lokacin ta yi bayani dalla-dalla kan yadda abinda ke cikin asusun masarautar da kuma yadda aka kasha kudin.

Ko da a wancan lokacin ma dai an fara binciken ne bayan wata rashin jituwa ta kunno kai tsakanin sarkin Kano da gwamnan Kano kan wasu kalaman da sarkin ya yi kan ‘yan siyasa.

Sai dai an warware sabanin a lokacin bayan da wasu manya suka shiga maganar.

To amma a wannan karon bayanai na cewa gwamnan Kano ya yi kunnen kashi ga duk masu kokarin shiga tsakani da nufin yayyafawa kurar da ta taso ruwa.

Har yanzu dai gwamnatin Kano ba ta fitar da matsayar ta kan shawarar da hukumar karbar korafe-korafe ta Kano ta bayar ba cewa a dakatar da Sarkin Kano Muhammad Sanusi II saboda zargin yana yin katsalandan a binciken kashe kudin masarautar ta hanyar hana duk wadanda aka gayyata domin bada shaida gaban hukumar.

Abin tambaya a nan shi ne shin ko a wannan karon ma sarkin na Kano zai tsallake wannan guguwar da ta taso, ko kuwa?

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...