Abin da ya sa Coronavirus ta fi kama jami’an gwamnatin Iran | BBC Hausa

Iran

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tun bayan da cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus ta barke a birnin Wuhan da ke China, kasa ta biyu da aka fi samun mace-mace sanadiyyar cutar ita ce Iran.

Hukumomin Iran dai sun ba da sanarwar mutuwar wani jami’i a majalisar da ke bai wa jagoran addinin kasar shawara.

Mohammad Mirmohammadi shi ne dai babban jami’i na farko da ya mutu sakamakon kwayoyin cutar corona, ko da yake akwai wasu da dama da aka tabbatar sun kamu da ita.

Mujtaba Adam wani Dan Nijeriya mazaunin birnin Tehran ya ce “akwai jami’ai biyu da suka kamu da cutar: na farko shi ne mataimakin ministan lafiya, na biyu kuma dan majalisar kare maslahar tsarin musulunci a Iran.”

“Mataimakin ministan lafiya ya kamu da wannan cuta tun da aikin harkar lafiya yake, dole ya zama ya na zuwa asibtoci da cibiyoyi na kiwon lafiya da wuraren da ake kula da wadanda suka kamu da cutar, hulda da jama’a shi ne sanadiyyar kamuwarsu da cutar.” a cewar mazaunin na birnin Tehran.

“Mutum na biyu Mirmohammadi mahaifiyarsa ce ta fara kamuwa da cutar ta coronavirus ta riga sa rasuwa shi kuma a ka sanar da mutuwarsa ranar Litinin.” a cewarsa.

Mujtaba Adam ya kara da cewa “kusan makwanni biyu da suka wuce, mahukunta kasar sun sanar da matakan da ya kamata dai-daikun mutane su dauka domin kare kansu daga kamuwa da cutar.”

“Kamar yadda a ka sani a ko ina ma shi ne tsafta, yawan wanke hannu da kuma nisantar shiga taruka na mutane.” in ji sa.

“Ta bangaren hukuma, sun samar da kayayyakin da ake bukata, sun ware asibitoci a garuruwa daban-daban wadanda a nan ne ake kula da mutanen da suka kamu da cutar,”

“Kusan ko da yaushe ana sanar da adadin mutanen da aka yi wa gwaji da wandanda suka kamu da cutar da wadanda suke warkewa da kuma wadanda suka rasu saboda kamuwa da cutar.” a cewarsa.

Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu mutum 66 sun mutu sakamakon cutar ta coronavirus.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...