Gwamnatin Najeriya ta bukaci Alkalin alkalan
kasar mai sharia Walter Onnoghen ya tsayar da
aikinsa kan zargin da yake da nasaba da kin bayyana
kadarorin da ya mallaka.
Wata sanarwa daga kotun da’ar ma’aikata, ta ce
a ranar Litinin 14 ga watan Janairu, Alkalin alkalan zai gurfana gabanta a wani mataki da ake ganin na kokarin tube shi daga mukaminsa. Jami’in hulda da jama’a na kotun da’ar ma’aikata, Ibraheem Al-Hassan, ya tabbatar wa da manema labaru da shari’ar da za a soma ta Alkalin alkalan.
Ana sa ran kotun da zai gurfana ita ce za ta tube shi daga mukaminsa domin kada ya yi katsalandan ga shari’ar.
Laifuka shida ake tuhumarsa, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Gwamnatin tarayya dai na zarginsa ne da saba wa dokar hukumar tabbatar da da’a ta Code of Conduct Bureau.
Rahotanni sun ce tun a ranar Juma’a aka sanar da shi kan lafiukan da ake zarginsa da kuma bukatar ya gurfana gaban kotu a ranar Litinin.