“Za Mu Iya Yi Wa Najeriya Addu’a a Nan, Ba Sai Saudiyya Ba” – Makinde Ya Soki Tafiyar Tinubu

Muhammadu SabiuHausa11 minutes ago



Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Advanced Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tafiyarsa zuwa ƙasar Saudiyya domin yi wa Najeriya addu’a.

Makinde ya bayyana cewa babu buƙatar shugaban ƙasar ya yi tafiya mai nisa zuwa Saudiyya domin yi wa Najeriya addu’a, alhali ana iya yin addu’ar a cikin ƙasar kuma Allah Ya amsa.

Gwamnan ya ce ya karanta a kafafen sada zumunta cewa Tinubu na shirin zuwa Saudiyya domin yi wa Najeriya addu’a, amma a ganinsa, shugabanni za su iya kasancewa a ƙasar tare da al’umma, suna roƙon Allah Ya kawo wa ƙasar mafita.

“Na karanta a kafafen sada zumunta cewa shugaban ƙasarmu zai tafi Saudiyya domin yi wa Najeriya addu’a. Ana amsa addu’a ko a cikin wannan ƙasar. Mu zauna a nan mu yi wa ƙasarmu da shugabanninmu addu’a,” in ji Makinde.

Ɗan takarar na APM ya kuma bayyana cewa shugabanci na gari yana buƙatar kasancewa tare da al’umma da kuma jin raɗaɗin matsalolinsu, maimakon yawan tafiye-tafiyen ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa idan shugaban ƙasa yana son yi wa Najeriya addu’a, zai iya yin hakan a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, a coci, masallaci ko kuma duk wani wuri a cikin ƙasar.

Makinde ya ce jam’iyyarsa ta APM ba za ta riƙa tafiye-tafiyen ƙasashen waje domin addu’a ba, sai dai za ta kasance tare da ’yan Najeriya wajen yi wa ƙasar da shugabanninta addu’a.

Wannan furuci na Makinde na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro, lamarin da ke jawo muhawara kan yawan tafiye-tafiyen jami’an gwamnati zuwa ƙasashen waje.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...