Sabbin Mutane Sama Da Dubu 102 Sun Kamu Da HIV A Najeriya A 2025



Wani rahoto da Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa an samu sababbin masu ɗauke da cutar HIV/AIDS sama da dubu 102 a faɗin ƙasar a shekarar 2025.

Rahoton mai taken “The State of the Health Nation Report” ya bayyana yadda cutar ta ƙaru a jihohin Najeriya 36 da kuma Abuja, inda ya nuna damuwa kan hauhawar alƙaluman duk da ƙoƙarin hukumomi na rage yaɗuwar cutar da mace-macen da ke da alaƙa da ita.

Haka kuma, bayanan hukumar NACA sun nuna cewa a yanzu akwai mutane kimanin miliyan 1.9 masu ɗauke da cutar HIV/AIDS a Najeriya.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]