Kotun Ƙolin Amurka Ta Yi Watsi Da Yunkurin Trump Na Dakatar Da Haihuwar ’Yan Ƙasa



Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da wani umarni da shugaban ƙasar Donald Trump ya nemi aiwatarwa domin kawo ƙarshen bai wa jariran da aka haifa a Amurka damar zama ’yan ƙasa kai tsaye.

Alƙalan kotun shida sun goyi bayan hukuncin, inda suka tabbatar da cewa haƙƙin samun ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa yana kunshe cikin kundin tsarin mulkin ƙasar. Sai dai wasu alƙalai uku sun nuna rashin amincewa da hukuncin.

Donald Trump ya bayyana matakin kotun a matsayin “abin takaici,” amma ya ce “Majalisar Dokoki za ta iya kafa doka akan hakan.”

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun yi maraba da hukuncin, suna masu cewa ya kare wani muhimmin hakki da kundin tsarin mulkin Amurka ya tanada.

A watan Afrilu ne Trump ya zama shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya halarci zaman Kotun Ƙoli yayin sauraron shari’a, duk da cewa ya bar kotun kafin a kammala zaman.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]