Mutum Biyar Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Neja



Akalla mutum biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a yankin Agaie da ke jihar Neja.

Jami’in Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Hussaini Guregi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce hatsarin ya rutsa da wata babbar mota mai ɗauke da fasinjoji da kuma tankar mai.

Rahotanni sun ce motar na kan hanyarta daga Gusau a jihar Zamfara zuwa Shagamu a jihar Ogun lokacin da hatsarin ya afku.

An bayyana cewa mutum biyar sun mutu nan take, yayin da aka kai waɗanda suka jikkata Asibitin Kwamishinan Agaie domin samun kulawar lafiya.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]