Gwamnatin Imo Ta Hana Sauya Littattafai Akai-Akai A Makarantu



Gwamnatin jihar Imo ta haramta yawan sauya littattafan karatu a dukkan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.

Haka kuma, ta dakatar da gudanar da bukukuwan yaye dalibai ga wasu matakai a tsarin karatu.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Farfesa BTO Ikegwuoha, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin rage wa iyaye da masu kula da yara nauyin kashe kudi a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, gwamnati ta umarci masu makarantu, shugabannin makarantu da malamai su bi wannan doka nan take, tare da gargadin cewa duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci mai tsauri, har da soke lasisi.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Æ™arÆ™ashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da Æ™arar da É—an majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]