Trump Ya Ce Amurka Na Yin Ƙoƙari A Yaƙin Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na ci gaba da yin “ƙoƙari” a yaƙin da take yi da Iran.

Trump ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Florida. Ya ce a cikin kwanaki uku kacal, sojojin Amurka sun nutsar da jiragen ruwan Iran guda 42 a cikin teku.

Shugaban ya kuma bayyana cewa zai kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan sojojin Amurka da suka mutu a yaƙin.

Ya ce sojojin da suka mutu sun zama “manyan jaruman ƙasarmu”, inda ya ƙara da cewa za a dawo da gawawwakinsu daga Iran cikin wani yanayi na daban.

Trump ya kuma jaddada cewa Amurka za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin mutuwar sojojinta ta “taƙaita”.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...