An Ga Jinjirin Watan Ramadan a Saudiyya

Haramain, wani gidan labarai na Saudi Arabia, ya tabbatar da cewa an hangi sabon watan Ramadan a kasar.

Bayan ganin watan, hukumomin Saudi sun sanar da cewa Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, zai kasance ranar farko ta wannan watan mai tsarki.

Haramain ta kara da cewa: “An hango watan Ramadan a Saudi Arabia. Saboda haka, Ramadhān 1447 zai fara a daren yau. Allah ﷻ ya karɓi azuminmu, sallolimmu da sauran ayyukan ibada, kuma ya ba mu damar amfani da lokutan wannan wata mai alfarma wajen aikata abin da yake faranta masa rai. Aameen.”

Watan Ramadan shi ne na tara a kalandar Musulunci kuma shi ne mafi tsarki a shekara.

More from this stream

Recomended