Ƴan sanda sun lalata masana’antar ƙera bindiga a jihar Benue

Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta ce jami’anta sun gano tare da lalata wata haramtacciyar masana’antar ƙera bindiga dake ƙauyen Shangev Tiev s ƙaramar hukumar Konshisha ta jihar.

Sewuese Aneneh mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benue ta faɗawa jaridar The Cable a ranar Laraba cewa jami’an sun kuma gano bindiga  AK-47 kirar gida, harsashi iri-iri, tukunyar iskar gas da sauran kayayyakin kira iri daban daban a yayin samamen da suka kai.

Mai magana da yawun rundunar ta jaddada irin kokarin da rundunar take na rage yawan haramtattun makamai a Benue ta ce an ɗauki matakan kamo mutanen da suka tsere a yayin samamen.

” Ta ce waɗanda ake zargin sun tsere lokacin da suka hangi ƴan sanda” a cewar  Aneneh .

A ranar 14 ga watan Janairu ƴan sanda sun gano wasu haramtattun masana’antun ƙera bindiga a kananan hukumomin Guma da Kwande a jihar.

More from this stream

Recomended