Mai shari’a Deinde Dipeolu ya bayar da umarnin kama wani mutum mai suna Oku bayan jami’in shigar da ƙara, Mohammed Bello, ya gabatar da buƙatar cewa Oku ya kasa halartar shari’ar duk da samun belinsa.
Rundunar ƴan sanda ta Sashen Yaƙi da Zamba (PSFU) da ke Ikoyi, Lagos, ta gurfanar da Oku tare da wasu mutane tara kan zargin damfarar masu jigilar man fetur na Dangote zuwa matatun Ibese da Obajana. Wadanda ake zargin sun haɗa da Ikechukwu Kingsley Obi, Chigozie Chrisogonus Osukwu, da wasu karin mutum bakwai.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun damfari kamfanin Dangote naira biliyan 19 tsakanin watan Janairu 2022 zuwa Yuni 2023.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 25 da 27 ga Fabrairu domin ci gaba da shari’a. Haka zalika, an umarci a kama Oku tare da tabbatar da gurfanar da shi gaban kotu.