Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta ce ta sallami jami’an ta uku da aka samu suna da hannu a kisan wani dalibin makarantar kimiya da Fasaha ta jihar.
A ranar 4 watan Satumba ne aka kashe dalibin mai suna,Quayum Ishola dake shekarar karatu ta biyu a fannin karatun difilomar fasahar wutar lantarki da kayan wuta.
Ishola wanda aka ce ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin sanadiyar tsinkewar a jijiyarsa bayan da jini ya yi ta kawararar daga wurin.
Ɗalibai sun gudanar da zanga-zanga ya zuwa hedkwatar rundunar ƴan sandan jihar Kwara inda suka buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar abokin karatun na su.
Ɗaliban sun yi iƙirarin cewa an harbe shi ne a wurin wani shingen binciken ababen hawa dake na ƴan sanda dake kan titin Panat-Shoprite a Ilorin.
A ranar 9 ga watan Satumba, Oluwimiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya ya sanar da sunayen ƴan sandan dake da hannun a lamarin da suka haɗa da Abiodun Kayode (inspector), James Emmanuel (inspector), da kuma sajan Oni Philip dukkansu daga sashen ayyukan yau da kullum na rundunar ƴan jihar.
A wata sanarwa ranar Juma’a, Adetoun Ejire-Adeyemi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kwara ya ce tuni aka tasa keyar ƴan sandan uku ya zuwa gidan yari.