10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaGwamnatin Katsina za ta samar da kantunan Rumbun Sauki

Gwamnatin Katsina za ta samar da kantunan Rumbun Sauki

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

Gwamnatin jihar Katsina ta shirya tsaf domin fara aiwatar da wani tsari na sayar da kayan amfanin yau da kullum akan farashi mai rahusa.

Sabon shirin zai ƙunshi samar da shaguna 38 da aka yiwa laƙabi da ‘Rumbun Sauki’  a fadin ƙananan hukumomin jihar 34.

Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda shi ne ya sanar da shirin samar da  kantunan a ƙananan hukumomin jihar bayan amincewar da majalisar zartarwar jihar ta yi a taron ta na 10.

Engr Yakubu Muhammad Danja mai bawa gwamnan jihar shawara kan bunƙasa tattalin arzikin karkara ya ce dukkanin wasu shirye-shirye sun kammala domin fara aiwatar da shirin.

Ya ce birnin Katsina zai samu ƙarin kantuna 2 a yayin da ƙananan hukumomin Funtua da Daura za su samu  karin kanti ɗaya -ɗaya.

Ya ƙara da cewa ana sa ran nan gaba za a faɗada shirin ta hanyar samar da kantunan a dukkanin mazaɓun jihar 361.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories