Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta koma sayar da mai a tsohon farashin kuɗin mai na watan Yunin shekarar 2023.
Kiran na TUC na zuwa ne biyo bayan ƙarin farashin kuɗin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi a baya bayannan.
Gabanin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu 2023 ana sayar da kowace litar mai kan kuɗi daga ₦195 ya zuwa 238 a sassa daban-daban na Najeriya..
Amma ƙarin da aka yi na kwanakin nan ya sa farashin litar mai ya koma ₦998 a Lagos da kuma 1,003 a Abuja.
Ƙungiyar masu gidajen mai ta danganta ƙarin kuɗin man fetur da ƙalubalen da ake fuskanta wajen shigo da man.
A wurin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, shugaban ƙungiyar TUC, Festus Osifo ya shawarci gwamnati da ta saka hannu a lamarin ta hanyar samar da dalar Amurka mai sauƙi ga matatar man fetur ta Dangote.
“Muna son farashin man fetur ya koma ƙasa da yadda yake a baya ba wai kawai ya koma yadda yake a da ba a’a ƙasa da haka,” ya ce.
Ya jaddada muhimmancin buƙatar gwamnati da ta bawa matatar Dangote canjin kuɗin ƙasashen waje akan ₦1000/$1 mai makon ₦1600 da ake sayar da dala ɗaya a yanzu.