EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba Darius Ishaku

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta kama Darius Ishaku tsohon gwamnan jihar Taraba kan zargin al-mundahanar kuɗaɗen da yawansu yakai biliyan 9.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Ishaku na can tsare a ofishin hukumar dake Abuja.

Duk da cewa mai magana da yawun hukumar ta EFCC ya tabbatar da labarin amma bai bada ƙarin gaske ba kan batun.

A ranar Alhamis ne hukumar ta EFCC ta shigar da ƙara a gaban  babban kotun tarayya dake Abuja inda takewa tsohon gwamnan tuhume-tuhume 15.

Ishaku ya mulki jihar Taraba daga shekarar 2015 ya zuwa 2023.

A cikin watan Yulin shekarar 2023 hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan kan binciken da take yi akan yadda ya mulki a jihar a tsawon shekaru 8 da ya shafe akan kujerar mulkin jihar.

More from this stream

Recomended