Mutanen da basu gaza 30 ba ne aka tabbatar sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru a jihar Kaduna a ranar Litinin.
Mutanen na kan hanyarsu ne ta zuwa garin Saminaka domin halartar bikin Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW).
A hirar da yayi kafar yaɗa labarai ta BBC, Ahmad Dayyabu wanda ya shirya taron Maulidin ya ce motar ta ci karo ne da wata babbar mota a kusa da garin Lere.
Wani jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna ya ce mutane 36 ne suka mutu a hatsarin.
Amma kuma Dayyabu ya ce yawan mutanen da suka rasu ya ƙaru zuwa 40 a yayin da wasu 30 ke cigaba da samun kulawa a asibiti.
“Sun taso daga garin Kwandare zuwa Saminaka. Lokacin da suka isa Lere sai motar da suke ciki ta ci karo da wata motar tirela,” ya ce.
Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa mutane 71 suke cikin motar lokacin da abuna ya faru.