Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama shugaban makarantar firamaren Gaidar Makada dake ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar kan zarginsa da ake na sayar da kayan makarantar.
A wata sanarwa mai ɗauke da sahannun, Kabir Abba Kabir mai magana da yawun hukumar da aka fitar ranar Asabar ta ce an kama shi ne bayan da aka bankaɗo wani tsari mai ban tsoro na yadda ake sayar da muhimman kayayyakin makarantar.
Ya ce hukumar na binciken lamarin kana ana cigaba da ƙoƙarin gano kadarorin da aka sayar.
” Bincike ya gano cewa kayayyaki masu muhimmanci kamar su ƙarafan kujeru da kuma katakon kujerun suna yin ɓatan dabo a makarantar.” A cewar sanarwar.
Sanarwar ta cigaba da cewa zargi ya faɗa kan shugaban makarantar wanda a baya sai da ƙungiyar iyayen yara da malamai ta PTA suka ɗora alamar tambaya akan yadda yake gudanar da aikinsa.
A yanzu dai hukumar ta mayar da hankali wajen gano kayayyaki tare da tabbatar da cewa irin wannan almundahanar bata kawo na kasu ba a harkar inganta ilimi.