Majalisar dokokin jihar Filato ta rage wa’adin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a jihar daga shekara uku zuwa biyu.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Mr Matthew Kwarpo ya faɗawa manema labarai ranar Laraba a Jos cewa an rage wa’adin ne domin da cewa da gyaran dokar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Filato ta shekarar 2024.
Ya ce rage wa’adin ya dace da bawa ƙananan hukumomi ƴancin gashin kai da aka yi kwanan nan a Najeriya ya ƙara da cewa ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kanke daga jam’iyar APC, Joseph Gokum shi ne ya gabatar da kuɗirin neman gyarar dokar kananan hukumomi ta shekarar 2017.
Kwarpo ya ce sanya gajeren wa’adi zai bada damar samar da lokacin gwajin da za a auna tasirin bawa ƙananan hukumomin yancin cin gashin kai.
Ya tabbatarwa da jama’ar jihar cewa an ɗauki matakin ne domin cigaban jihar ba wai dan biyan buƙatun wasu mutane ba.