Ƴan bindiga sun kashe mutane 6 a Benue

Aƙalla mutane shida aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka  kai ƙaramar hukumar Agatu ta jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum guda aka kashe  a garin Iwari a yayin da aka kashe sauran mutane biyar ɗin ranar Juma’a a Olegagbane.

Wani mutum mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce

” Maharan dake ɗauke da makamai sun kai farmaki jiya a Iwari inda suka kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

“A ranar Juma’a 23 ga watan Agusta ƴan bindigar sun farma Olegagbane a inda suka kashe wasu mutane biyar, “

Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Philips Ebenyakwu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce maharan sun kasance masu aikata kisa, sata da kuma ɓarna kana su tsere.

Ya ce bayan sun tafi suna kuma sake dawowa su kai farmaki suyi kisa  an kuma kasa gano dalilinsu na yin haka.

Ebenyakwu ya kuma bayyana ƙalubalen da suke fuskanta na kula da mutanen hare-haren ya raba da gidajensu.

More from this stream

Recomended