Ƴan Fashin Daji Sun Sace Matar Wani Dagaci Da Ƴaƴansa Biyu A Kaduna

An shiga zaman zullumi a ƙauyen Galadimawa dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan da ƴan bindiga suka farma ƙauyen tare da ɗauke matar dagacin garin da ƴaƴansa biyu.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:30 na dare a cewar wasu majiyoyi dake yankin, waɗanda aka ɗauke su ne matarsa, Fatima Aliyu da kuma ƴaƴansa Abdullahi Aliyu da Kamal Aliyu.

Ƴan fashin dajin sun isa ƙauyen ne su da yawa inda suka riƙa harbin kan me uwa da wabi domin tsorata mutane kafin su fasa katanga su shiga gidan dagacin.

Hussaini Umar mai riƙe da sarautar, Sarkin Fadar Galadimawa ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Ya ce an ji maharan na neman Dagacin abun da ke nuni da cewa shi suka zo yin garkuwa da shi amma ba su same shi ba.

Mallam Umar ya ƙara da cewa maharan sai da suka bincike ko ina a gidan  har cikin silin amma basu Ganshi ba.

Bayan da suka gaza samunsa ne shi ne suka sace matarsa da ƴaƴansa.

Ya roƙi gwamnati ta kawo masu ɗauki saboda yadda suke yawan fuskantar hare-hare daga ƴan bindiga.

More from this stream

Recomended