Mutane 3 sun mutu a wani gini da ya rufta a Lagos

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos ta ce ma’aikatan gini uku ne suka mutu bayan da wani gini ya rufta a yankin Maryland dake birnin na Lagos.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa babban sakataren hukumar ne ya tabbatar da haka a ranar Alhamis cikin wata sanarwa.

Ya ce lamarin ya faru ne a  gida mai namba 13 dake kan titin Wilson Mba a rukunin gidaje na  Arowojobe  dake Maryland da misalin Æ™arfe uku da rabi na dare.

Ya Æ™ara da cewa wasu Æ™arin ma’aikata uku aka samu damar zaÆ™ulowa inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

More from this stream

Recomended