Mutane 3 sun mutu a wani gini da ya rufta a Lagos

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos ta ce ma’aikatan gini uku ne suka mutu bayan da wani gini ya rufta a yankin Maryland dake birnin na Lagos.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa babban sakataren hukumar ne ya tabbatar da haka a ranar Alhamis cikin wata sanarwa.

Ya ce lamarin ya faru ne a  gida mai namba 13 dake kan titin Wilson Mba a rukunin gidaje na  Arowojobe  dake Maryland da misalin ƙarfe uku da rabi na dare.

Ya ƙara da cewa wasu ƙarin ma’aikata uku aka samu damar zaƙulowa inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

More from this stream

Recomended