Gamayyar kungiyoyin ƙwadago za su sake ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a cikin kwanaki bakwai domin cigaba da tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi.
Da take magana da ƴan jaridar dake fadar shugaban ƙasa a ranar Alhamis, Nkiruka Onyejeocha ƙaramar ministar ƙwadago ta bayyana ƙwarin gwiwa cewa nan bada jimawa ba za a warware batun dambarwar mafi ƙarancin albashin.
Ministan na magana jim kaɗan bayan ganawar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya shugabannin kungiyar ƙwadago ta NLC da TUC.
Festus Osifo shugaban ƙungiyar TUC ya ce ganawar ta su ta mayar da hankali kan abubuwan da suka damu ƴan Najeriya.
Joe Ajaero shugaban ƙungiyar NLC ya ce ba wai an tattauna batun naira da kwabo a’a magana ake tsakanin naira 250,000 da kuma 62,000 a haka za a tsaya har sai an kawo ƙarshen tattaunawar.