An yi taron addu’a a Jigawa kan rashin tsaro da matsin rayuwa

Wata kungiyar jin ƙai mai suna Sawaba Humanitarian Initiative ta gudanar taron addu’a na musamman domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da tattalin arziki dake wahalar da ƴan Najeriya.

An gudanar da taron addu’ar ne a Dutse babban birnin jihar Jigawa bayan da duk ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na hana taron ya ci tura.

Daruwan-Ɗaruwan mutane da suka halarci taron addu’ar sun bayyana damuwarsu kan makomar ƙasarnan dai-dai  lokacin da yunwa, cututtuka da talauci ke cigaba da kashe mutane a kullum a yayin da waɗanda suke kan mulki a ke cigaba da nuna ko-in-kula kan halin da ake ciki.

Da yake magana bayan taron addu’ar, shugaban ƙungiyar Sawaba Humanitarian Initiative na ƙasa, Kwamared Umar Ɗanjani Hadejia ya ce halin da ake ciki na nema yafi ƙarfin talaka.

“Sai da na kasa riƙe hawaye bayan da naga yadda yunwa take wahalar da tsofaffi da yara ar ƙauyukan Jigawa,”

“Babu ɗan siyasa mai hankali da zai yi bacci lafiya bayan ganin abun da na gani a ƙauyuka da dama,” ya ce .

Ya ce za gudanar da irin wannan addu’ar a ƙananan hukumomin jihar.

More from this stream

Recomended