Israel Ayeni ɗantakar gwamnan jihar Ondo ƙarƙashin jam’iyar NNPP ya janye daga takarar da yake yi.
A ranar 16 ga watan Nuwamba ne aka shirya gudanar da zaɓen gwamnan jihar.
26 ga da watan Afrilu ita ce ranar da aka gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyar ta NNPP inda Ayeni ya kayar da abokin karawarsa a zaɓen Ibrahim Ajagunna da kuri’a 100.
A wasikar yanje takarar ta sa da aka fitar ranar Laraba a Akure babban birnin jihar, ɗantakar ya ce matakin da ya ɗauka shi ne zai amfani jam’iyar.
Peter Olagookun shugaban jam’iyar NNPP na jihar Ondo ya ce Ayeni ya janye takarar ne a ƙashin kansa domin jam’iyar ta samu damar tsayar da ɗantakara nagartacce.
Olagookun ya ce za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na maye gurbin ɗantakar a ranar Laraba.