Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa laifukan da suka shafi tattalin arziki da kuma kudi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ana sanar da jama’a cewa Yahaya Adoza Bello (tsohon gwamnan jihar Kogi), wanda hotonsa ya bayyana a sama hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na nemamsa ruwa a jallo bisa zargin karkatar da kudade har N80,246,470,089.88.
“Bello, dan shekara 48, ɗan kabilar Ebira ne kuma dan asalin karamar hukumar Okenne ne ta jihar Kogi.”