Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun


Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da aka kama daga sassan jihohin Legas da Ogun a ranar Talata.

Hakan ya faru ne a Ibereko Badagry, Legas, bisa bin umarnin kotu.

Brig.-Gen.  Shugaban Hukumar Buba Marwa (Rtd), ya bayyana muhimmancin tallafin da jama’a ke da shi ga kokarin da ake na yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya.

Jami’an NDLEA ne a sassa daban-daban na jihohin Legas da Ogun daga watan Janairun 2022 har zuwa yau, musamman daga tashoshin jiragen ruwa na Legas, da filayen jiragen sama, da kan iyakokin kasa suka ƙwace wadannan kayayyaki.

More from this stream

Recomended