EFCC ta kama yan damfara a Abuja

Hukumar EFCC dake yaki da masu yi wa tattalina arzikin kasa ta’annati ta samu nasara kama wasu mazabanta ta hanyar Intanet wadanda aka fi sani da yan Yahoo-Yahoo.

Jam’ian hukumar na shiyar Abuja su ne suka samu nasarar kama mutanen a yankin FO1 dake Kubwa a Abuja biyo bayan bayanan sirri da suka samu kan ayyukansu.

Mutanen da aka kama su 9 sun hada da kalu Kennedy Ndukwe, Onyenso Emmanuel, Richard Yakubu, Haruna Abubakar, Peter Ukabam, Godwin Peters, Usuman Garba Haruna, Nwani Chukwuma da kuma Kabiru Shehu.

Kayayyaki daban-daban aka samu a hannun mutane da suka hada da laptop da wayoyin hannu.

More from this stream

Recomended