Bayern Munich za ta karɓi baƙwancin Barcelona inda za a buga wasan ba tare da ƴan kallo ba a gasar Champions League a ranar 8 ga watan Disamba a daidai lokacin da ake samun ƙaruwa a adadin masu kamuwa da korona a Bavaria.
A farkon wannan makon ne Shugaban Bavaria, Markus Soder ya bayyana cewa akwai yiwuwar a ɗauki irin wannan matakin, inda ya ce “ƙwallon ƙafa na da rawar da take takawa matuƙa”.
Bayern Munich ta samu nasara a matakin sili ɗaya ƙwale inda ta zama zakara a rukunin E, da kuma karawa tsakanin Barcelona da kuma Benfica domin zuwa mataki na biyu a cikin 16 na ƙarshe.
Barcelona za ta je gaba muddin ta samu nasara.
Sai dai idan aka yi kunnen doki ko kuma aka doke ta, hakan zai ba Benfica nasara a matakin sili ɗaya ƙwale gabannin Barcelona da nasara a ɓangaren Dynamo Kiev.
An ci Barcelona 3-0 a wasanta da Bayern a Nou Camp a watan Satumba, haka kuma zuwan su na ƙarshe zuwa Allianz Arena an ta shi 3-2 a zagayen kusa da na ƙarshe a wasan zagaye na biyu da suka buga a Maris ɗin 2015.
Sai dai Barcelona ta wuce zuwa wasan ƙarshe sakamakon nasarar da ta samu ta 3-0 inda ta doke Juventus a wasan ƙarshe wanda hakan ya sa ta ɗauki kofin Champions League na biyar kuma shi ne na baya-bayan nan.