Ana zargin sojoji da lalata da mata don basu abinci a Tigray

Tigray

An bada rahoton samun zarge-zarge masu karfi na cin zarafin mata a yankin Tigray na arewacin Habasha, ciki har da laifin fyade a garin Mekelle, in ji wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafi yayin yaki.

Sojojin gwamnati sun kwace iko da Mekelle, babban birnin yankin, a ranar 28 ga Nuwamba bayan an kwashe makonni ana fada.

Misis Patten ta ce “Akwai kuma rahotanni masu tayar da hankali na mutanen da ake zargin an tilasta musu yi wa danginsu fyade, bayan an musu barazana.

“Wasu rahotanni sun ce wasu sojoji ma sun tilasta wa mata yin lalata da su kafin basu abinci.

“Duk da yake cibiyoyin kiwon lafiya sun nuna karuwar bukatar hana daukar ciki na gaggawa da kuma gwajin cututtukan da ake yadawa ta hanyar jima’i (STIs) wanda galibi hakan manuniya ce ta cin zarafin da aka samu” inji ta.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniyar ta ce akwai kuma karin rahotanni na cin zarafin mata da ƴan mata a wasu sansanonin’ yan gudun hijira.

Firai minista Abiy Ahmed ya kaddamar da farmaki ta kasa da ta sama a ranar 4 ga Nuwamba don fatattakar jam’iyya mai mulki a yankin, bayan da dakarunta suka kame sansanonin sojan tarayya.

Ya ayyana nasara a Tigray bayan rikicin wata guda, amma shugabannin kungiyar ta TPLF wadanda suka gudu sun lashi takobin ci gaba da yakin.

Babu cikakken bayani dangane da mutum nawa aka kashe a rikicin, sai dai a baya Shugaban Habasha Mista Abiy yace sojoji ba su kashe farar huka ko daya ba lokacin yakin da ya kai ga tumbuke TPLF daga mulki.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi kira a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen da duka bangarorin ke wa juna, ciki har da yi wa fararen hula kisan kiyasahi da harbe-hare da sace-sace a yankukuna fararen hula da asibiti.

Fiye da mutum 50,000 sun tsallaka Sudan don gujewa rikicin.

Yakin ya barke ne a farkon watan Nuwamba, yayin da Firaminista Abiy Ahmed ordered ya bai wa sojoji umarni su kaddamar da hare-hare kan dakarun yankin Tigray.

Ya ce ya yi hakan ne a matsayin martani kan wani hari da aka kai wa wani sansanin sojoji da dakarun gwamnatin ke ciki a Tigray.

Rikicin ya zo ne bayan watanni da samun sabani tsakani gwamnatin Abiy da shugaban TPLF – jam’iyyar da ta mamaye yankin.

Jam’iyyar ta shafe kusan shekara 30 ana damawa da ita a gwamnatin kasar, kafin Mista Abiy ya jinge ta bayan ya hau mulki a 2018, yayin da ake tsaka da zanga-zanagr kin jinin gwamnati.

More from this stream

Recomended