
Asalin hoton, Twitter/Gov Kad
Wasu na zargin Gwamna El-Rufai da rashin daukar kwakkwaran mataki kan ‘yan bindigar
Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta tabbatar da sace wasu malamai da kananan yara daga cikin Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa kwalejin dirar mikiya ranar Asabar, inda suka sace malami daya da kuma yara biyu.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kuma harbi wani malamin, yana mai cewa yanzu haka yana jinya a asibiti.
“Wadannan ‘yan bindiga sun je Nuhu Bamalli Polytechnic ne jiya [Asabar] da dare, inda suka sace malami daya da yara biyu na wani malamin sannan suka harbi wani malamin,” a cewarsa.
Kwamishinan ya kara da cewa an baza jami’an tsaro domin gano inda wadanda aka sace suke.
Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa musamman a yankin na Zaria, inda a kwanakin baya rahotanni suka ce an sace wasu mutane bayan kashe wata matar aure.
Raddi daga masu amfani da Twitter
Satar malamin da yara biyu ta janyo hankalin masu amfani da shafin Twitter a Najeriya, wadanda suka rika sukar gwamnatin jihar bisa abin da suka ce rashin mayar da hankalinta kan tsaron jihar.
Zahrah Kumbo, wadda ‘yar jihar ta Kaduna ce, ta soki Gwamna Nasir El-Rufai bisa “kasa tabbatar da tsaro a Zaria da ma jihar Kaduna amma da haka kake yunkurin tursasa wa baligai biyan haraji a jihar nan.”
Ta kara da cewa “ya kamata ya yi gaggawar kai musu agaji kafin a sace dukkansu mazauna Zaria”.
Shi ma Deji Adeyanju ya yi wa gwamnan tambaya yana mai cewa: “Yaushe za ka je Zaria ka saka kuka kamar yadda ka yi a Lagos mako biyu da suka wuce?”
Shi ma wani da ke ikirarin shi ma’aikaci ne a Kwalejin ta Nuhu Bamalli mai suna Blackeee a shafin Twitter ya shaida wa gwamnan cewa: “Mu ma’aikatan Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria ba mu da kwanciyar hankali! Su ma daliban makarantar ba su tsira ba! Ya kamata tsaronmu ya zama abin da ya fi muhimmanci a gare ka, ba kawai makaranatar ba, har da Kaduna…
Sai dai Kwamishinan Tsaron Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewa gwamnatinsu tana bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaro amma lamarin yana da alamar zagon-kasa.
“Wadannan sace-sace suna ta’azzara ne saboda akwai masu tsegunta wa ‘yan bindiga domin su zo su sace mutane,” in ji shi.
A cewarsa, galibin masu satar mutanen suna shigowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da jihar Kaduna su yi satar sannan su fice, yana mai karawa da cewa sun daura damarar magance matsalar.