
—BBC Hausa
Shugaba Muahhamdu Buhari ya sassauta dokar kulle a jihohin Abuja da Legas da Ogun.
Sassaucin zai fara daga karfe 9:00 na safiyar Asabar 2 ga watan Mayu.
Ya ce: “Duba da wannan da kuma shawarwarin kwamitin fadar shugaban kasa na musamman da ke yaki da korona da kungiyar gwamnoni, na bayar da umarnin sassauta matakan kulle a Abuja da Legas da Ogun daga ranar Asabar 2 ga watan Mayun 2020 daga karfe 9 na safe.
“Burinmu shi ne mu samar da tsari da zai tabbatar da cewa tattalin arzikinmu ya ci gaba da aiki a yayin da a hannu guda kuma za ku ci gaba da daukar tsauraran matakai kan yaki da annobar cutar korona. “Wadannan matakai irin su ne shugabannin kasashe suka dauka a fading duniya.