
Kwamitin Shugaban Kasa na kula da yaki da cutar Coronavirus, Covid-19, sunce ce har yanzu basu karbi ko naira daga cikin tallafin da wasu kamfanoni suka bayar ba don yakar cutar Corona Virus ba kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.
Lai Mohammed, mamba a kwamitin kuma Ministan Labarai da Al’adu ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a lokacin da yake magana da manewa labarai don ba da cikakken bayani game da ayyukan kungiyar a kokarinta na yaki da cutar.
Mista Mohammed ya nuna rashin jin dadinsa game da kiraye-kirayen da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke yi na neman a binciki kwamitin a kan kwashe kudaden da aka tara daga masu bada Gudummuwar.
Har yanzu ba mu samu kobo guda daya ba; mutane suna son a bincike mu kan yadda muke kashe kudaden da ba mu gani ba. Inji shi.