
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
‘Yan sanda na neman kama wani daga cikin masu zanga-zanga
An yi dauki ba dadi tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Musulmin China a birnin Hong Kong.
Daruruwan masu zanga-zanga a Hong Kong sun yi gangamin nuna goyon baya ga Musulmi ‘yan kabilar Uighur da ake musgunawa a China.
Mutanen na zargin hukumomin China da tura dubban Musulmai ‘yan kabilar Uighur zuwa wasu sansanonin da ta kira na sake ilmantarwa.
Masu zanga-zanga da suka ce suna goyon bayan Musulmin sun kuma nuna fargabar samun kansu a irin halin da Musulman Uighur ke ciki.
Sun ce suna neman kawo karshen abin da suka kwatanta da karfa-karfar da China ke yi a gabashin Turkestan da sauran yankuna.