Israila ta kaddamar da sabbin hare-hare kan mayakan Falasdinu bayan da aka samu sabbin hare-haren roka daga Gaza kwana daya bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kafafen watsa labaran Falasdinawa sun ce makamai masu linzami sun fada kan wasu wurare mallakar kungiyar mayaka ta Palestinian Islamic Jihad (PIJ) da safiyar Juma’a, abin da ya janyo raunata mutum biyu.
Hakan dai na zuwa ne bayan harba wa Israi’la wasu makaman roka ranar Alhamis, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar PIJ ta ayyana.
Rikici tsakanin Israila da Falasdinawa dai ya kara rincabewa bayan da Israila ta kashe babban kwamandan kungiyar PIJ ranar Litinin.
Isra’ila ta ce Baha Abu al-Ata ‘hadari’ ne kasancewarsa mutumin da ya kitsa kai wa Israila harin roka na baya-bayan daga Gaza.
Fiye da rokoki 450 ne aka harba kan Israila, inda ita kuma ta kaddamar da hare-haren sama a kan Gaza a kwanaki biyu da suka kwashe suna fafatawa.