Unicef: Cutar Pneumonia ta fi kisan kananan yara a Najeriya | BBC news

Pneumonia na yin kashe yara a duk kasa da dakika 39 a duniya

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Pneumonia na yin kashe yara a duk kasa da dakika 39 a duniya

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce a kowacce shekara cutar pneumonia na kashe kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Rahoton hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce Najeriya ce kasar da Pneumonia ta fi kashe kananan yara a duniya.

Rahoton ya nuna yadda ciwon ke sanadin kashe yara masu kasa da shekara biyar fiye da duk wani ciwo.

Alkalumman Unicef kan Cutar na 2018 sun nuna cewa kimanin yara 18 ke mutuwa duk sa’a daya sakamakon cutar Pneumonia.

Rahoton ya kuma ce daga cikin adadin yaran da suka mutu a 2018 a Najeriya, kashi 19 sun mutu ne sakamakon Pneumonia.

  • Tsohon minista ya karkatar da kudin kiwon lafiya
  • Amnesty ta gargadi gwamnatin Buhari kan kisan jama’a

Cutar da ta shafi huhu, Unicef ta ce matsaloli da suka shafi karancin abinci mai gina jiki da shakar hayakin itace da ake konawa wajen dafa abinci ne ke haifar da cutar ga yara kanana.

Baya ga Najeriya daga cikin kasashen da cutar ta fi tsanani, sun hada da Indiya da Pakistan da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da kuma Habasha.

A watan Janairu ne kungiyoyi da hukumomi za su gudanar da taron duniya a Spain domin tattauna cutar Pneumonia da ke kisan yara.

Jerin kasashen da cutar Pneumonia ta fi tsanani

Hukumar Unicef ta bayyana jerin kasashen da cutar pneumonia ta fi kisan yara ‘yan kasa da shekara biyar a 2018.

1. Nigeria 162,000

2. Indiya 127,000

3. Pakistan 58,000

4. Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo 40,000

5. Habasha 32,000

6. Indonesia 19,000

7. China 18,000

8. Chadi 18,000

9. Angola 16,000

10. Tanzania 15,000

11. Somalia 15,000

12. Nijar 13,000

13. Mali 13,000

14. Bangladesh 12,000

15. Sudan 11,000

Jimilla a duniya 802,000

More from this stream

Recomended