‘Yan Bindiga Sun Kashe Sama Da Mutane Goma A Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane goma tare da raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai yankin Yar Center dake kauyen Sherere a karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina.

Kamar yadda wani ganau ba jiyau ba ya bayyanan, ‘yan ta’addan sun shigo yankunan ne a jiya Lahadi a kan babura inda da isar su suka budewa jama’a wuta kafin daga bisani suka kona shaguna da ababen hawa dake wajen.

More from this stream

Recomended