An kama mataimaki shugaban karamar hukuma saboda alaka da ‘yan bindiga

Sojoji dake aikin kakkabe yan ta’adda a jihar Zamfara da a kaiwa lakabi da Operation Sharar Daji sun kama mataimakin shugaban karamar hukumar Anka,Yahuza Ibrahim Wuya kan zarginsa da ake da alaka da masu garkuwa da mutane.

An kama shine ranar 13 ga watan Afirilu bisa dogaro da kwararan bayanan sirri da aka samu dake nuna alakarsa da barayi masu garkuwa da mutane a garuruwan Wuya da Sunke a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta Operation Sharar Daji, Manjo Clement Abide ya fitar.

Ana zargin Yahuza Ibrahim yana taimakawa wajen sayar da shanu da jakunan da aka sace da kuma samarwa da barayin bayanai kan ayyukan jami’an tsaro da kuma yan banga.

“Ana kuma zarginsa da taimakawa wajen kubutar da wani kasurgumin mai sayar da bindigogi mai suna Sani Yaro daga gidan yarin Gusau,” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended