Ƴan ta’adda sun kai mummunan hari a Jihar Taraba

An kai Taraba wani mummunan hari a ƙauyen Ganfeto da ke Unguwar Daka na karamar hukumar Bali, ta jihar Taraba wanda ya kai ga rasa rayuka 10.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mutanen garin na cikin tashin hankali da kaduwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya tabbatar da wannan mummunan labari a cikin wata sanarwa da aka yi wa manema labarai a ranar Laraba a Jalingo, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a gano wadanda abin ya shafa ba.

Ya kuma nuna cewa ba a tabbatar da cewa maharan ‘yan fashi ba ne.

More from this stream

Recomended