Ƴan Kenya sun fusata da tsarin tilasta biyan ‘bashi da wahala’

A man holds the new Kenyan bank notes in circulation on June 28, 2019, in Nairobi. - Kenya is withdrawing the old notes to crack down on embezzlement and tackle a wave of counterfeit.

Asalin hoton, AFP

Cikin jerin wasikun da muke samu daga Æ´an jaridar Afirka, É—an jaridar Kenya Waihaga Mwaura ya yi nazari kan yadda masu bayar da bashi ke fusata jama’a ta hanyar tsoratarwa a kokarin karbo bashin da aka bayar ta hanyar manhajar bayar da lamuni.

Wani fasto ya kawo ziyara ɗakinmu na watsa labarai a Nairobi babban birnin Kenya ya gabatar da ƙorafi.

Tsawon mako ɗaya, an dame shi da kiran waya daga masu bibiyar bashi waɗanda suka yi iƙirarin cewa ɗaya daga cikin mabiyansa ta bayar da sunansa a matsayin garanto kan bashin da ta karɓa.

Da farko ya dauki al’amarin a matsayin almara amma bayan damunsa da kira ya fusata kan wannan tsarin na bashi.

Yawan tattaunawar waya sai sauyawa take a kullum.

Da farko masu kiransa sun kasance masu ladabi da nuna biyayya inda suka roƙe shi ya tattauna da mabiyarsa don ta biya bashin da ta karɓa a watan da ya gabata.

Amma daga baya masu kiran wayar sun koma masu zafi har ma da suka, inda suka kira shi faston jabu wanda ya kaucewa bayyana gaskiya game da bashin da mabiyansa suka kasa biya tare da alkawarin damunsa da kiran waya.

Sun ƙara fusata shi inda suka soki matarsa a lokacin da ta yi ƙoƙarin shiga tsakani.

An shafe kwanaki faston ba ya amfani da wayarsa saboda ya ki amincewa da bukatun masu kiransa.

Kuma bayan hirar da aka yi da shi da kuma tattauna batun a kafofin sada zumunta na intanet, Æ´an Kenya da dama sun ci gaba da bayyana irin abin da ya faru da suna cin karo da masu bibiyar bashin.

ÆŠaya daga cikin masu amfani da Twitter ya ce an yi masa gargaÉ—in cewa “Idan ba ka biya ba, za mu cire maka Æ™oda.”

Wata kuma ta ce ta taÉ“a rancen 2,000 na kudin Kenya ($18), bayan kwana 10, “suka dame ni. Na kasa bacci ko tunani, Na sha zagin da ba a tunani.”

Na ukun ya bayyana yadda ya yi aiki a matsayin mai bibiyar bashi, dole ya cimma wa’adi da abin da aka kayyade masa.

“Ba su damu da yadda za ka dawo da kuÉ—in ba. KuÉ—i ne kawai abin da ya fi damunsu. Dole na daina yin aikin don tsira da mutunci na,” in ji shi.

Rancen kuÉ—i ta manhajar salula

Ƴan Kenya sun rungumi tsarin karɓar rance ta wayoyin salula da intanet.

Ya fi tsari da kuma sauƙin samu ba tare da wata jingina ba.

Amma a ciki akwai matsala ga masu ba da bashi waɗanda ke amfani da halayen masu karɓar rancen don auna cancantarsu ta bashi ba tare da kuma sun haɗu da su ido da ido.

Tabbas wannan ba zai yiwu ba idan nahiyar Afirka ba ta kasance jagora a duniya ba na harakar kudi a manhajar wayar salula ba.

Kamfanonin sadarwa na wayoyin salula sun mamaye hda-hadar kudi tsawon shekara 10.

Sun fi mayar da hankali kan gibin É“angaren lamuni inda masu karamin karfi ba su da damar samun bashi saboda rashin aiki da babu bukatar jingina ko masu ba da lamuni.

Amma shigowar su kasuwar Afirka ya ja hankali saboda galibinsu ba a kayyade su ba, kuma saboda yadda ake ganin salon kasuwanci na daban.

Sun ja hankalin matasa tare da jefa su cikin damuwa da wuri kuma kamfanonin suna kunyatar da su ta amfani da dabarun da ba a saba gani ba idan sun kasa biya.

Kuma yayin da ƴan Kenya ke hanzarin karɓar bashi wasu sun bayyana damuwa kan yawan kudin ruwan da ake zabgawa.

Yayin da kudin ruwa matsakaici na bashin banki bai wuce tsakanin kashi 12 zuwa 14 a shekara, a manhajar salula ya kai tsakanin kashi 75 zuwa 395 a shekara.

Rancen kuÉ—in sayen gida a manhajar salula

Bugu da ƙari ana zargin wasu kamfanonin bayar da bashin musamman ɗaya daga cikinsu kamfanin China da ake zargi da tursasa biyan bashi cikin kwana 30, yayin da kuma Google da ya samar da manhajojin ya bukaci a biya bashin cikin kwana 60.

Amma shugaban kungiyar masu bayar da bashi a hanyoyin intanet, Kevin Mutiso ya kare mambobinsa inda ya ce matakan da ake bi ya taimaka masu kananan masana’antu samun rance cikin sauri.

Ya ce idan da babu bashin Æ´an Kenya da dama ba za su shiga wani hali lokacin kullen korona tsawon shekara É—aya

Mutane sun yi ƙoƙarin samun kuɗin da za su saye abinci da biyan kudin haya da sufuri da kuma biyan kuɗin makarantar yara, in ji shi.

Yayin da wasu ke ganin mutunta Æ™a’ida ta fi muhimmanci don magance matsalolin masu bayar da bashi, wasu kuma suna fargabar cewa tabbatar da bin Æ™a’ida za ta iya hana masana’antun da suka samar da ayyuka da zuba jari a tattalin arzikin da annobar korona ta karya

A cewar wasu masu sa ido a tattalin arzikin, nan ba da jimawa ba rancen kudin mallakar gidaje za ta koma ta wayoyin salula.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...