Akalla mutane uku ne aka kashe, yayin da wasu sama da 51 ciki har da wani hakimi aka yi garkuwa da su a wasu sassan jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki kauyen Bagega, wani kauye mai hakar ma’adinai a jihar, inda suka yi ta harbe-harbe a kai a kai, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutanen kauyen uku.
Rundunar ƴan sanda ba ta ce komai a kan lamarin ba saboda jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar, bai amsa kiran da aka yi masa ba.
Sai dai Sarkin Kauyen Malam Abubakar Uba ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters faruwar lamarin.
Ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da hakimin yankin kafin su ci gaba da yin garkuwa da mutane da dama a kauyen.