Rahotanni na cewa ƴan bindiga sun sace dalibai da kawo yanzu ba a san yawan adadinsu ba akan babbar hanyar east-west a ƙaramar hukumar Ughelli ta jihar Delta..
A cewar jaridar The Cable ɗaliban dake cikin mota ƙirar Sienna na kan hanyarsu ta dawowa daga birnin Calabar ne na jihar Cross River lokacin da aka farma motar ta su da yammacin ranar Juma’a.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Delta,Bright Edafe shi ne ya tabbatarwa da jaridar faruwar haka a ranar Litinin.
Edafe ya ce jami’an ƴan sanda na bin sawun masu garkuwar domin kuɓutar da ɗaliban.
Lamarin ya shiga jerin ƙarin yawan ɗaliban da aka yi garkuwa da su a Najeriya.