Ƴan bindiga sun kashe likita a Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Dr Stephen Angbas, mamallakin asibitin Lafia-Angbas.

Mummunan lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a lokacin da Angbas ke kan hanyarsa ta zuwa gonarsa a kan babur da ke karamar hukumar Awe a jihar Nasarawa.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne, sun kai wa Angbas da wani ɗan Okada mai rakiyar sa hari.

Wani babban jami’i daga karamar hukumar, Mista Ibrahim ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin.

Ya kuma nuna cewa shugaban ƙungiyarsu ya sanar da hukumomin tsaro domin su shiga lamarin cikin gaggawa.

More from this stream

Recomended