Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda 4 A Ebonyi

Ƴan bindiga sun kai farmaki kan rukunin wasu jami’an ƴan sanda dake aikin sintiri a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi inda suka kashe huɗu daga ciki .

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe biyar na ranar Juma’a a wurin shingen binciken ababen hawa na gadar  Ebyia dake kan titin Hill Top a Abakaliki.

An kuma kashe fararen hula biyu a lokacin da ake musayar wuta tsakanin ƴan sandan da kuma yan bindigar.

Joshua Ukandu mai riƙon muƙamin kakakin rundunar yan sandan jihar ya ce ana zargin cewa ƴan bindigar mambobi ne na ƙungiyar IPOB dake fafutukar samar da ƙasar Biafra.

“Ƴan sandan sun yi musayar wuta sosai da ƴan bindigar a musayar wutar ne ɓatagarin suka gudu har suka bar bindiga guda ɗaya,” Ukandu ya ce.

Ya ƙara da cewa ƴan sanda na cigaba da bibiyar ƴan bindigar.

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...