Ƴan sanda sun kama malamin makaranta saboda zargin yi wa budurwa fyaɗe

An kama wani malamin makarantar sakandire a jihar Ogun, Lateef Olaniran bisa zargin yi wa wata budurwa fyade.

Olaniran, dan asalin karamar hukumar Ipokia ta jihar Ogun, malamin lissafi ne a makarantar Ebenezer Grammar School, Iberekodo, Abeokuta.

Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Adijat Olaleye ce ta bayyana hakan a ranar Laraba.

A cewarta, an kama Olaniran ne a ranar Asabar, a lokacin da wata ‘yar tawagarta ta samu waya daga wata budurwa, inda ta ce wani mutum ya yi mata fyade.

Kwamishiniyar ta ce ma’aikatar ta dauki matakin ne inda ta nemo wanda abin ya faru da ita, wadda ta ce ta je dakin gwaje-gwaje domin yi mata gwaje-gwaje daban-daban kafin daga bisani aka kai ta ofishin ‘yan sanda ta kai rahoto.

“Daga baya mun tafi tare da ‘yan sanda zuwa gidan wanda ake tuhuma amma bayan ƙwanƙwasa masa, ya ki bude kofar. Mun sami ɗan’uwan ga mai gidan wanda ya taimaka mana muka shiga harabar,” in ji ta.

More from this stream

Recomended