Ƴan bindiga sun saki yaron da suka yi garkuwa da shi na tsawon shekaru 2

Masu garkuwa da mutane sun sako yaro na karshe Treasure Ayuba da suka yi garkuwa da shi a makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna bayan shafe shekaru biyu da watanni hudu a hannunsu.

Treasure na cikin dalibai 121 na makarantar Baptist da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Yuli 2021 a kauyen Maraban Damishi a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

An ce an sake shi a ranar Juma’a tare inda tuni ya koma ga ƴan’uwansa.

A halin da ake ciki gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana farin cikinsa da samun ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamna Sani ya bayyana jin dadinsa ga jama’a da hukumomi da suka jajirce wajen yin kokari da addu’o’i na ganin an dawo da wanda aka sace.

More from this stream

Recomended