
Wasu yan bindiga a Zamfara sun yi garkuwa da wasu matasa da suka kammala jami’a akan hanyarsu ta zuwa sansanin yan yiwa kasa hidima dake jihar Kebbi.
Matasan sun fito ne daga jihar Akwa Ibom.
Eddy Megwa daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NYSC dake Abuja shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Megwa ya ce anyi awon gaba da matasan ne da daddare a Zamfara lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin da aka tura su a jihar Kebbi.
Uku daga cikinsu sun samu nasarar tserewa a lokacin da yan bindigar suka tsare su.
Megwa ya kara da cewa yanzu haka shugaban hukumar ta NYSC yana Zamfara domin lalubo hanyar da za a kuɓutar da su.