Ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan takarar gwamnan Filato

0

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Filato a zaɓen 2019, Nkemi Nicholas Nashe.

Mista Nashe wanda jigo ne a Jam’iyyar PDP, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙaramar Hukumar Shendam a baya.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa wani makusancin Mista Nshe ɗin na cewa jama’ na zaman ɗar-ɗar tun bayan faruwar wannan lamari a Shendam.

Shi kansa gwamnan jihar mai ci a yanzu Simon Lalong ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Shendam.

Sace Mista Nshe na zuwa ne ƙwanaki kaɗan bayan sakin wani basarake a jihar ta Filato da aka sace, Charles Mato Dakat.

Sai dai sojoji da ke jihar sun bayyana cewa sun kama mutum takwas da suke zargi da hannu a sace basaraken.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here